Lafiya Zinariya: Hanyoyin da ke taimaka wa masu cutar basur

August 2024 ยท 2 minute read

15 Mayu 2021

Bayanan sauti

Lafiya Zinariya: Hanyoyin da ke taimaka wa masu cutar basur

Latsa hoton da ke sama don sauraren shirin:

Zuwa bandaki a kan kari domin yin bayan-gida na daga cikin hanyoyin da ke taimaka wa masu cutar basur.

Hakan dai na kunshe ne a wata makalar da aka sake wallafawa a watan Agustan, 2020 a mujallar kiwon lafiya ta cibiyar koyar da ilimin likitanci na jami'ar Havard da ke Amurka.

Haka kuma cikin shawarwarin da makalar ta bayar na hanyoyin magance cutar cikin sauki sun hada da zama a ruwan dumi wanda aka zuba gishiri.

Sannan da cin abinci mai dauke da fibre da motsa jiki kamar tattaki na mintoci 20 zuwa 30 a rana.

Zama a kan kujera ko mazauni mai taushi maimakon mai karfi shi ma yana taimaka wa masu cutar ta basur.

Hakan a cewar makalar yana taimakawa wajen rage kumburin basur din tare da hana wasu sabbi fitowa.

Ta kuma kara da cewa ana gano wannan cuta cikin sauki idan mutum ya je asibiti an duba shi, musamman idan basir din mai tsiro ne.

Haka kuma cikin gwaje-gwajen da za a yi sun hada da duba wa ko basur din yana fitar da jini.

Kuma idan yana jinin sai an tabbatar da cewa ba wata cuta ce ta janyo zuban jinin ba, wato kamar cutar daji, musamman idan mutum ya haura shekaru 45 a duniya.

ncG1vNJzZmivp6x7o67CZ5qopV%2Bdrra%2FwGiqoaGirrJuv8eiqbKdXaOubrnUrJimpZGjenaDkGlscHFi